IQNA

Sheikhul Azhar: Lokacin Haihuwar Annabi (SAW) Shi Ne Lokacin Farin Ciki Mafi Girma

16:37 - October 18, 2021
Lambar Labari: 3486440
Tehran (IQNA) Sheikh Ahmad Al-Tayyib babban malamin cibiyar ilimi mafi girma ta Ahlu Sunnah a duniya ya ce; bikin maulidin Manzon Allah (SAW) shi ne mafi girma a cikin dukkanin bukukuwa da suke dauke da kamala ta dan adam.

Sheikh Ahmad Al-Tayyib, Sheikh Al-Azhar, ya ce bikinmu na tunawa da zagayowar lokacin  haihuwar cikamakin annabawa, babu kamarsa a cikin dukkanin bukukuwa na murna ga musulmi.

A cikin jawabinsa a wani biki a jajibirin ranar haihuwar Annabi wanda shugaban kasar Masar  Abdel Fattah al-Sisi da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar suke halarta, Sheikh Ahmad Tayyib ya jaddada cewa, ranar zuwan manzon Allah duniya, ita ce babbar rana ta zuwan mafificin halitta mafi soyuwa da daukaka a wurin Allah a kan dukkanin talikai, a kan haka wanann rana ce mai matsayi da daraja a wurin dukkanin masoya manzon Allah (SAW) na hakika.

A kan haka ya ce, wanann rana ce ta tunatar da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, kan matsayin fiyayyen halitta, da kuma ambatar kyawawan halayensa da ya koyar da dan adam, wanda kuma wannan yana cikin dabi'ar annabawa da manzanni, wadanda Allah ya kare su daga karkacewa da fitintinu na shaidanu, kuma ya cika dabi'unsu na waje da na ciki da gaskiya da alheri da rahama.

 

4005845

 

captcha