IQNA

Taron Tunawa ‘Yan Aljeriya Da Faransa Ta Kashe A Babban Masalacin Aljiers

22:33 - October 17, 2021
Lambar Labari: 3486439
Tehran (IQNA) Taron tunawa da kisan gillar da aka yi wa 'yan Aljeriya 4000 da sojojin Faransa suka yi a karni na 19.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin karni na 19, kusan masu bauta 4000 ne a Aljeriya da ke zanga -zangar mayar da Masallacin Katshawe zuwa coci, sojojin mulkin mallaka na Faransa suka kashe a babban birnin kasar ta Aljeriya.

An gina masallacin ne a lokacin Daular Usmaniyya, Masallacin Katshawe da ke Aljeriya ba kawai daya ne daga cikin muhimman alamomin kasar ba, har ma da muhimmin abubuwa da ke a matsayin shaida kan laifukan gwamnatin mulkin mallaka ta Faransa a Aljeriya.

A wata hira da manema labarai na cikin gida, shugaban Aljeriya Abdel Majid Tebon ya gabatar da rahoton hukuma kan kisan kiyashin da aka yi wa masallata  kusan dubu hudu a lokacin mulkin mallaka 1830-1962.

 

4005662

 

captcha