IQNA

Ministan Saudiyya Ya Bayyana Cewa Sun Kawar Da Masu Tsattsauran Ra'ayi Daga Kan Mimbarori

22:27 - September 21, 2021
Lambar Labari: 3486336
Tehran (IQNA) Minista mai kula da harkokin addini a kasar Saudiyya ya sanar da cewa sun kawo gagarumin sauyi a cikin lamarin wa'azi a kasar

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Abdullatif Al; Sheikh Minista mai kula da harkokin addini a kasar Saudiyya ya sanar ad cewa sun kawo gagarumin sauyi a cikin lamarin wa'azi da ma sauaran jawabai na addini da ake gabatarwa a kasar.

Rahoton ya ce, a zantawarsa da tashar MBC, Minista mai kula da harkokin addini a kasar Saudiyya ya bayyana cewa, a halin yanzu kasar ta dauki salo na sassaucin ra'ayi da kuma fada da tsattsauran ra'ayin rikau na addini.

ya ce yanzu abin da yake a gaban ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar shi ne yada sassaucin ra'ayi, kuma wannan yana a cikin kur'ani da hadisan ma'aiki (SAW).

A kan haka ministan ya ce, ma'aikatarsa ta dauki kwaran matakai na sanya ido da kuma bin kadun dukkanin bayanai da malamai suke yi a wuraren wa'azi da hudubobin Juma'a da lamurra da suka shafi addini.

Haka nan kuma ya kara da cewa, an samar da tsari guda daya wanda dole ne dukaknin malamai da masu wa'azi da limaman ju'ama su yi  aiki da shi a fadin kasar, domin tabbatar da cewa an kawo karshen yada tsattsauran ra'ayin rikau kan addini.

Wannan dai yana daga cikin sabon salon siyasar Muhammad Bin Salman Yarima mai jiran gadon sarautar kasar ta Saudiyya, wanda yake da ra'ayi da ke karkata ga turawan yamma.

 

3998852

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: karshen tstsauran
captcha