IQNA

Cibiyar Darul Ifta Ta Masar Ta Fitar Da fatawar Haramta Rubuta Kur'ani Da Haruffan Latin

18:02 - September 20, 2021
Lambar Labari: 3486329
Tehran (IQNA) babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta fitar da fatawar haramta rubuta kur'ani mai tsarki da haruffan Latin.

Jaridar Alwatan ta kasar Masar ta bayar da rahoton cewa, a jiya babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta fitar da fatawar haramta rubuta kur'ani mai tsarki da haruffan Latin a madadin na larabci.

Bayanin cibiyar ya ce, kamar yadda aka saukar da kur'ani a cikin harshen larabci, saboda haka rubutunsa ma haka yake  a cikin haruffan larabci, amma tarjama ko fasasra za a iya yi da kowane harshe, amma ba rubutun haruffan wani harshe na daban ba.

Wani marubuci dan kasar Masar ne ya kirkiro salon rubutun kur'ani da haruffan latin, ta yadda wadanda suke a  wasu kasashe na duniya da suke son karanta kur'ani amma ba za su iya karanta haruffan larabci ba, za su iya karanta shi kamar yadda yake a  cikin larabci amma da haruffan latin.

Amma fitar da wannan fatawa ya kawo karshen wannan aiki a kasar Masar, domin tuni aka saka wannan bayania  dukkanin shafuka na fatawoyin muslucni a  fadin kasar .

 

 

 

3998708

 

Abubuwan Da Ya Shafa: haruffan latin
captcha