Jagoran juyin juyin juya halin muslunci na kasar Iran ya bayyana nuna rashin amincewa da halascin Isra’ila a wuraren wasanni na duniya abu ne mai matukar muhimmanci.
A yayin da yake ganawa da ‘yan wasan kasar Iran da suka nuna kwazo wajen wasannin motsa jiki na Olympics da kuma na motsa jiki na nakasassu, Jagoran juyin juyin juya halin muslunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da irin namijin kokarin da suka yi wajen ciwo wa kasarsu lambobin yabo na zinariya da azurfa da kuma tagulla a bangarori daban-daban da aka gudanar da gasar wasannin.
Ya ce kwazon da suka nuna ya tabbatar da irin kishin kasa da suke da shi, da kuma sanya buri a cikin zukatan sauran matasan kasar, kan cewa za su iya kai wag a irin wannan matsayi a nan gaba matukar suka sanya himma da kwazo.
Dangane da mata ‘yan wasa na kasar Iran ad suka halarci wannan gasa kuwa, ya bayyana cewa babban abin burgewa dangane da lamarinsu shi ne, yadda suka gudanar da dukkanin wasanni tare das aka tufafin muslunci, wanda ko shakka babu hakan zai kara karfafa gwiwar wasu daga cikin kasashen musulmi wajen kiyaye lamarin sutura ga mata masu sha’awar shiga gasar wasanni.
A lokacin da yake yin tsokaci kan matakin da wasu ‘yan wasa daga wasu kasashen musulmi suka dauka na kin yin wasa tare da ‘yan wasan Isra’ila kuwa, ya bayyana cewa wannan babban abin jinjina ne ga wadanan ‘yan wasa, domin daukar irin wannan mataki na nuna rashin halascin Isra’ila a wurare na tarukan kasa da kasa abu ne mai matukar muhimmanci.