IQNA

Iran Ta Zama Mamba A Kungiyar SCO A Hukumance

18:34 - September 17, 2021
Lambar Labari: 3486318
Tehran (IQNA) kasar Iran ta zama mamba a kungiyar bunkasa harkokin tattalin arzikin Shanghai Cooperation Organization.

An bude taron kasashen kungiyar SCO ko Shanghai Cooperation Organization karo na 21 a birnin Doshambe na kasar Tajakisatn, inda shugaban kasar Chaina Jinping ya fada wa taron cewa kungiyar ta karbi kasar Iran a matsayin mamba na dindindin a cikinta.
 
Kungiyar SCO dai mai kasashe 8 tabbatattu da kuma kasashe 4 masu sanya ido ta bude taronta na 21 ne tare da halattar shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi, sanna shugaban kasar Cana ya gabatar da jawabinsa na kafar bidiyo.
 
Sauran shuwagabannin kungiyar ta suka sami halartar taron sun hada da na Tajakistan, Kyrqizistan, Kazakistan, Belarus, Pakistan, Turkmenistan, da kuma Uzbekistan.
 
Har’ila yau kasashen Masar Qatar da kuma Saudiya suna da matsayin yan kallo a kungiyar. Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya na fada a jawabinda da ya gabatar a taron kan cewa lamuran al’adu ne suka fi zama abinda ya hada kasashen na SCO, kuma daga nan yakamata kasashen su fara aiki tare.
 

 

 

captcha