IQNA

Zaman Karbar Gaisuwar Ayatollah Hakim A Tsakanin Hubbarori Biyu Na Karbala

17:43 - September 12, 2021
Lambar Labari: 3486299
Tehran (IQNA) ana ci gaba da zaman karbar gaisuwar Ayatollah Sayyid Hakim Babban malami da Allah ya yi masa rasuwa a Iraki

Tashar Alkafil ta bayar da rahoton cewa, ana ci gaba da zaman karbar gaisuwar Ayatollah Sayyid Hakim Babban malami da Allah ya yi masa rasuwa a Iraki kwanaki tara da suka gabata.

Bayan ga zaman majalisin karbar gaisuwa a Najaf, ana wani majalisin a Karbala tsakanin hubbaren Imam Hussain (AS) da Abul Fadl (AS).

Ayatollah Sayyid Muhammad Said Hakim yana daga cikin manyan malaman mazhabar Ahlul bait (AS) wanda ya rasu a ranar Juma'ar wancan makon da ya gabata, sakamakon tsayawar zuciya.

 

3996864

 

captcha