IQNA

Wakilai Daga Kasashe 85 Za Su Halarci Taron Duniya Kan Fatawa A Kafofin Sadarwa Na Zamani

21:58 - July 25, 2021
Lambar Labari: 3486137
Tehran (IQNA) wakilan kasashe 85 ne za su halarci taron kasa da kasa kan fatawa a kafofin sadarwa na zamani.

Shafin yada labarai na jaridar Alwafd ya bayar da rahoton cewa, Ibrahim najm mataimakin babban mai bayar da fatawa na kasar Masar ya bayyana cewa, an kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da taron fatawa ta hanyar kafofin sadarwa na zamani.

ya ce a halin yanzu dai wakilan kasashe 85 ne za su halarci taron na kasa da kasa kan fatawa a kafofin sadarwa na zamani da zai gudana a ranakun 2 da kuma 3 ga watan Agusta mai kamawa.

Taron wanda na karawa juna sani ne, zai samu halartar masana daga wadannan kasashe, wadanda za su bayyana mahangarsu dangane da hanyoyin da ya kamata a kyautata lamarin fatawa ta hanyoyi na zamani, domin musulmi su amfana da hakan cikin sauki a duk inda suke a duniya.

Baya ga haka kuma a zaman za a tattauna hanyoyin da suka dace domin fitar da fatawoyi da suke a kan hanya, domin yi wa matasa saiti wadanda akan yaudare su tare da saka su cikin ayyukan ta'addanci da sunan addini.

 

3986095

 

 

captcha