IQNA

Dan Wasan Judo Na Aljeriya Ya Ki Amincewa Ya Yi Wasa Da Bayahuden Isra'ila A Wasannin Olympics Na Japan

18:08 - July 23, 2021
Lambar Labari: 3486131
Tehran (IQNA) Fathi Nurain dan wasan kasar Aljeriya ne a bangaren wasannain Judo wanda yaki amincewa ya yi wasa da bayahuden Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran SAFA ya bayar da rahoton cewa, a jiya Fathi Nurain dan wasan kasar Aljeriya ne a bangaren wasannain Judo wanda yaki amincewa ya yi wasa da bayahuden Isra'ila a wasannin Olympics na Japan.

Wannan na zuwa ne bayan kada kuri'ar da aka yi a bangaren wasan Judo, inda zai kara da Muhamamd Abdulrasul dan kasar Sudan a zagayen farko, idan har ya samu nasar, to karawa ta gaba zai hadu da bayahuden Isra'ila ne.

Ganin haka a nan take Fathi Nurain ya sanar da cewa ya janye daga gasar baki daya, saboda ba zai hadu da bayuhuden Isra'ila ba.

Ammar Bin Yakhluf Mai horar da 'yan wasan Judo a kasar aljeriya ya bayyana cewa, Fathi Nurain ya janye ne domin nuan rashin amincewa da zaluncin da Isra'ila take yi a kan al'ummar Falastinu, tare da haramta musu hakkokinsu  a cikin kasarsu.

Wannan dai ba shi ne karin farko da Fathi Nurain yake daukar irin wannan mataki ba, domin kuwa ko a cikin shekara ta 2019 ya janye daga wasananin UAE, kasantuwar akwai bayahuden Isra'ila a cikin wasan a bangaren Judo, domin kada su hadu da juna.

 

3985810

 

 

captcha