IQNA

Kwafin Kur'anai Na Tarihi A Babban Cibiyar Ajiyar Kayan Tarihi Ta Louvre

22:05 - July 13, 2021
Lambar Labari: 3486102
Tehran (IQNA) Cibiyar ajiyan kayan tarihi ta Louvre ita ce wurin ajiyar kayan tarihi mafi girma a duniya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an nuna wasu daga cikin kwafin kurnai mafi jimawa a babbar cibiyar ajiyar kayan tarihi na duniya da ke birnin Paris an kasar Faransa.

Bayanin ya ce, akwai dukaknin nau'oin kayan tarihi daga sassa daba-daban na duniya da ake ajiye da su a wannan wuri, wadanda aka kawo su kasar Faransa daruruwan shekaru da suka gabata.

daga cikin abubuwan da aka nuna a wurin na kayan tarihi, har da wasu kwafin kur'anai wadanda tarihinsu ke komawa zuwa daruruwan shekaru masu yawa.

Wadannan kur'aai dai tarihinsu na komawa zuwa ga karnonin da sarakunan Abbasiyawa suka yi mulki, ko kuma lokutan da sarakunan daular Usmaniya suka yi mulki.

Yanzu haka dai wannan wuri yana karbar dubban mutane da suke zuwa domin duba kayan tarihi daga ciki da wajen kasar ta Faransa.

 

3982948

 

captcha