Shafin yanar gizo na Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, ya ce za’ayi wa Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, allura ta farko ta rigakafin cutar korona wacce aka samar a kasar samfurin (CovIran Barekat) a cikin kwanaki masu zuwa.
Shafin khamenei.ir ya nakalto Dakta Alireza Marandi, shugaban kwalejin koyon aikin likita na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana bayyana hakan a jiya Laraba.
“Wannan allurar rigakafin sakamako ne na kokarin matasa masana kimiyyar Iran’’ in ji Marandi.
Dr. Marandi ya ce tun da jimawa ya kamata a yi wa Jagoran allurar rigakafin toh sai dai Jagoran ya ce shi yana so ne a yi masa allurar rigakafin da aka samar a cikin gidan Iran din ba wanda aka shigo da ita daga waje ba.
Ya kara da cewa samar da rigakafin ya sanya Iran ta zama kasa ta shida a duk fadin duniya da ta samu wannan nasarar bayan Indiya, China, Birtaniya, Amurka, da Rasha.
Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta amince da allurar rigakafin ta Iran a cikin gaggawa a farkon wannan watan.