IQNA

Netanyahu Ya Kidime Bayan Kayar Da Shi Inda Ya Sha Alwashin Kifar Da Sabuwar Gwamnatin Yahudawa

22:52 - June 14, 2021
Lambar Labari: 3486011
Tehran (IQNA) Tsohon firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, zai ci gaba da yin duk abin zai iya domin ganin cewa sabuwar gwamnatin Isra’ila ba ta kai labari ba.

A cikin rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, Netayahu ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin da aka kafa a Isra’ila gwamnati ce ta ha’inci, wadda Iran take farin ciki da ita, domin kuwa a cewarsa Iran ta san cewa wannan sabuwar gwamnati tana da rauni, ba kamar gwamnatinsa ba.

Ya ce yana sanar da Iran da Hizbullah cewa su kwana da sanin cewa zai dawo kan kujerar firayi ministan Isra’ila nan ba da jimawa ba, kuma zai dawo da shirinsa domin tunkarar barazanar da suke yi wa yahudawan Isra’ila.

Sai masana da dama suna ganin cewaabubuwa da dama ne suka taru wadanda suka bai wa Naftali Bennett damar kayar da Netanyahu, mafi muhimmanci daga ciki shi ne batun tuhumarsa da cin hanci da rashawa, halasta kuadden haram da kuma zamba cikin aminci.

Kasantuwar Netanyahu ba shi da kariya a yanzu, hakan zai bai wa bangaren shari’a damar gurfanar da shi a gaban kuliya cikin sauki domin gabatar da wadannan tuhumce-tuhumce a kansa.

Sai dai kuma wasu suna ganin cewa Netanyahu mutum ne wanda ya kware wajen shirya makirci da makida ta siyasa, wanda zai iya yin komai a rayuwarsa domin cimma burinsa.

 

3977319

 

captcha