Shafin yada labarai na jaridar Alkhalij ya bayar da rahoton cewa, dakin karatu na Kalba a yankin Sharijah a hadaddiyar daular larabawa ya bude wani baje kolin kur'anai rubutun hannu.
A wannan baje kolin kur'anai ana nuna wasu kwafin kur'anai da aka rubuta daruruwan shekaru da suka gabata a cikin tsarin rubutu mai kyau mai kayatarwa.
Rahoton ya ce a wurin ana nuna kwafin kur'anai kimanin guda 40, wadanda mafi yawansu an rubuta su ne a lokacin daular Usmaniya ta Turkawa, wato daruruwan shekaru ad suka gabata.
Alhimadi shi ne shugaban baje kolin, ya kuma bayyana cewa, an samo wadannan kwafin kur'anai ne daga kasashe daban-daban, inda aka tara su wuri guda domin nuna su a wannan baje koli, wanda yake samun mahalarta daga ciki ciki da wajen kasar.