IQNA

Yunkurin Isra'ila Na Kisan Wani Kwamandan Hamas Bai Yi Nasara Ba

18:52 - May 19, 2021
Lambar Labari: 3485930
Tehran (IQNA) yunkurin Isra'ila na kisan wani kwamandan dakarun Qassam reshen soji na Hamas a gaza bai yi nasara ba.

A cikin kimanin mako guda da ya gabata da sojojin yahudawan sahyuniya suka kwashe suna yin kisan kiyashi kan musulmi mazauna zirin Gaza, Isra'ila ta yi yunkuri na kisan wani kwamandan dakarun Qassam reshen soji na Hamas a Gaza amma ba ta samu nasara ba.

Majiyoyin sojojin yahudawan ne da kansu suka sanar da hakan, inda suka ce sun yunkurin kashe wasu amnyan kwamnadoji na kungiyoyin gwagwarmayar falastinawa su shida zuwa bakawai, musamman ma dai Muhammad Daif, amma hakan bai yi nasara ba.

A daya bangaren kuma banda yankunan zirin Gaza da kuma yamma da kogin Jordan, rahotannin sun bayyana cewa a jiya Talata tashe-tahsen hankula sun game sauran yankunan Falasdinawa da aka mamaye wadanda suka hada da garin Nablus.

A halin yanzu ana rigingimu a dukkan yankunan Falasdinawa da aka mamaye, inda falasdinawa suke nuna goyon bayansu ga mutanen zirin Gaza wadanda aka fi kashewa, sannan su ne suke maida martani ga gwamnatin yahudawan sahyoniyya da makamai masu linzami.

Ya zuwa yanzu dai yawan wadanda suka yi shahada a cikin kwanaki kimani 9 da suka gabata sun kai mutane 213, 61 daga cikinsu yara kanana ne, sannsan 36 kuma mata. Har’ila yau akwai wasu 1,442 kuma suna jinya.

Har’ila yau a wani labarin kuma ministocin harkokin waje na kungiyar tarayyar turai sun gudanar da taro ta yanar gizo a jiya Talata, inda suka bukaci bangarorin da suke fafatawa a Falasdinu su tsagaita budewa juna wuta, sannan su san cewa hanyar diblomasiyya ce kadai za ta warware matsalolin da ke tsakaninsu.

 

3972397

 

 

captcha