IQNA

Tilawar Mamhud Anwar Shuhat Daga Surat Quraish

22:31 - August 10, 2020
Lambar Labari: 3485073
Tehran (IQNA) Mahmud Shuhat Muhammad Anwar makarancin kur'ani ne daga Masar da ya karanta surat Quraish da kyakkyawan sautinsa.

Mahmud Shuhat Muhammad Anwar ya yi amfani da salon tilawa a mataki na tilawar tangimi mai kayatarwa.

An haife shi a ranar 10 ga watan Satumban 1984 a garin Mait Ghamar da cikin gundumar Diqhaliyya  a kasar Masar, kuma ya yi karatu ne a hannun mahaifinsa, inda ya hardace kur'ani tun yana dan shekaru 12 da haihuwa.

A halin yanzu yana da shekaru 36 a duniya, kuma ya ziyarci kasashe da dama domin gabatar da karatun kur'ani da kyakkyawan sautinsa, da suka hada da Iraki, Kuwait, UAE, Qatar, Iran, Bahrain, Pakistan, Syria, Indonesia, Belgium, Amurka, Faransa, Afirka ta kudu, Turkiya, Girka, Aljeriya, Maldev.

3915767

 

captcha