Shafin alahad ya bayar da rahoton cewa, da yammacin yau Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da jawabi a yau wanda zai fara daga misalin karfe 17:30 na yamma agogon birnin Beirut.
A cikin jawabin nasa ana sa ran Sayyid Nasrullah zai tabo muhimman lamurra ne dangane da abin da ya shafi hatsarin da auku a birnin Beirut, da kuma matsayar Hizbullah kan hakan, da ma sauran lamurra da suka shafi yankin gabas ta tsakiya.