IQNA

Shafin kwafin Kur’ani Mai shekaru 1300 A Baje Kolin Littafai na Sharijah

23:56 - November 01, 2019
Lambar Labari: 3484213
An nuna wani shafin kur’ani da aka rubuta tun kimanin shekaru 1300 da suka gabata a Sharijah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin albayan cewa, an nuna wannan shafin kwafin kur’ani wanda yak e dauke da ayoyi 72 zuwa 75 surat Anfal, dakuma aya ta 1 zuwa 9 a cikin surat Taubah.

Masu bincike sun gudanar da kwakwaran bincike a kan wannan shafi na kur’ani, kuma sun gano cewa ya kai shekaru 1300 da suka gabata da rubuta shi.

Bisa ga abin da masu binciken suka bayyana, sun ce an rubuta kur’anin ne tun karni na takwas miladiyya, tsakanin shkara ta 714 zuwa 740.

Abin tuni a nan dai shi ne, an fara gudanar da taron baje kolin littafai an kasa da kasa a Sharijah tun kimanin shekaru talatin da takwas da suka gabata, kuma an fara waann shekara ne tun ranar Laraba da ta gabata.

 

 

 

3853732

 

 

captcha