IQNA

An kame Wasu Na Shirin Kai hari Kan Masu Ziyarar arbaeen A Iraki

23:57 - October 16, 2019
Lambar Labari: 3484160
Jami’an tsaron kasar Iraki sun bankado wani shirin kai harin ta’addanci a kan masu ziyarar arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga saumaria News cewa, a jiya Jami’an tsaron kasar Iraki sun bankado wani shirin kai harin ta’addanci a kan masu ziyarar arbaeen a yankin Biji a kan hanyarsu ta zuwa Karbala.

Bayanin ya ce an kame mutane 10 wadanda dukkaninsu ‘yan ta’addan Daesh ne dauke da bama-bamai a cikin sahun masu tafiya ziyarar arbaeen, kuma wasu daga cikinsu manya ne a cikin kungiyar, inda suke da nufin aiwatar da wani mummunan kisa a kan masu ziyarar.

Baya ga haka kuma an kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan bayan da asirinsu ya tuno a lokacin da suke shirin tayar da jigidar bama-bamai a tsakiyar masu tafiya ziyarar arbaeen acikin lardin Salahuddin da ke arewacin Iraki.

Jami’an tsaron kasar Iraki sun ce sun kammala dukkanin shirinsu domin bayar da tsaro ga masu ziyarar, a kan dukkanin hanyoyin da suke isa zuwa birnin Karbala.

 

3849960

 

 

 

captcha