IQNA

Turkiya Ta Fara Kai Harin A Arewacin Syria

23:51 - October 09, 2019
Lambar Labari: 3484138
Bangaren kasa da kasa, Erdodan ya sanar da fara kai hari a arewacin Syria a yau.

Kamfanin dillancin labaran iqna, gwamnatin kasar Turkiyya ta sha alwashin ci gaba da kutsawa cikin arewacin kasar Syriya don share mayakan kungiyar kurdawa daga yankunan da suke iko da su a kasar ta Siriya, duk tare da kiraye-kirayen da kasashen duniya suke mata na ta janye daga kasar ta Siriya.

Shugaban kasar ta Turkiya Rajab Tayyeed Erdogan ya ce dole ne sai ya samar da tsaro a wasu yankuna na arewacin kasar ta Siriya inda zai sake tsugunar da yan gudun hijirar kasar kimani miliyon 4 da suke cikin kasar Turkiyya a halin yanzu.

Sai dai kungiyar tarayyar Turai ta bayyana damuwarta da wannan shirin na gwamnatin kasar Turkiya, saboda yi yuwar yan gudun hijiran da basa son komawa cikin kasar Siriya zasu yi kokarin yin hijira zuwa kasashen na turai.

A nata bangaren gwamnatin kasar Rasha ta yi kira ga kurdawan kasar Siriya na kungiyar su shiga tattaunawa kai tsaye da gwamnatin kasar Siriya don samar da hanyar warware halin da suka fada ciki.

 

3848868

 

captcha