Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa,
jagoran kiristoci mabiya darikar katolika Paparoma Francis a lokacin ganawa da
shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya bukaci Iran da ta taka rawa wajen
warware matsaloli na siyasa da fataucin makamai da ta’addanci a yanking abas ta
tsakiya baki daya.
Ganawa tsakanin bangarorin biyu ta
zo a ziyarar aiki da shugaban kasar Iran yake gudanarwa akasar Italiya, inda ya gana manyan jami’an
gwamnatin kasar, da suka hada da takwaransa na kasar ta Italiya.
A yau ne shugaba Hassan rauhani zai
bar kasar ta Italiya, domin kama hanya zuwa kasar Faransa.