IQNA

Amuka Ba Za Ta Iya Kutsawa Cikin Tsarin Makaman Kariya Na Iran Ba

23:53 - June 24, 2019
Lambar Labari: 3483767
Bangaren siyasa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya karyata da'awar da Amurka ke yi na cewa ta kai hari kan tsarin makaman kariya na Iran a yanar gizo.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya fadi yau cewa, babu gaskiya a zantukan da jami’an gwamnatin Amurka suke yi dangane da kai wa Iran harin yanar gizo, tare da bata tsarin shirin makamanta na kariya a cikin yanar gizo.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yau a birnin Tehran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka na da’awar cewa ta kai hari na yanar gizo a kan tsarin tsaron kasar Iran, musamman abangaren makaman kariya masu linzami na Iran, ya ce wannan tsabar karya ce.

Ya ce tsarin makaman kariyar na Iran tsari ne wanda Amurka ba ta san yadda aka gina shi ba, kuma ba ta da masaniya kan yadda ake sarrafa shi, akan haka kuma ba ta san yadda za ta iya bata shi ba.

Sayyid Musawi ya kara da cewa, duk da irin matakan tsokana da Amurka take dauka, Iran ba za ta fara kaddamar da yaki a kan wata kasa ba, amma kuma a lokaci guda a shirye take ta kare kanta da dukaknin karfinta.

Ya cehar kullum Iran tana mika hannu ga sauran kasashen yankin, da su hada karfi da karfe tare domin samun zaman lafiya a yankin gabas tsakiya, tare da kare yankin da al’ummarsa, amma wannan kira bai samu karbuwa daga wasu kasashen yankin ba.

Ya ce a maimakon haka ma, irin wadannan kasashe suna fifita yin kawance da Amurka da Isra’ila domin rusa Iran da ma wasu daga cikin kasashen larabawa wadanda basa dasawa da su, ya ce wannan ba maslaha ce ta al’ummar wannan yanki ba, kamar yadda kuma ba maslaha ce ga gwamnatocin da suka zabin yin haka ba.

3821859

 

captcha