IQNA

Paparoma Ya Jaddada Wajabcin Yin Mu'amala Da Musulmi

23:59 - June 22, 2019
Lambar Labari: 3483763
Bangaren kasa da kasa, shugaban mabiya addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Francis ya jaddada wajabcin tattaunawa da kuma yin mu'amala da musulmi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi a jami'ar Katolika da ke fadar vatican a jiya, shugaban mabiya addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Francis ya jaddada wajabcin tattaunawa da kuma yin mu'amala da musulmi a ko'ina cikin fadin duniya, musamman ga mabiya addinin kirista.

Ya ce wajibi ne ga dukkanin daliaban da suke koyon ilmomi na addinin kirista su samu masani kan addinin muslunci da kuma addinin yahudanci, domin sanin yadda za su yi mu'amala da dukkanin mabiya wadannan addinai tare da girmama abubuwan da suka yi imani da su.

A shekarar da ta gabata ce paparoma ya gana da baban malamin ciyar Azahar, inda suka cimma matsaya kan ci gaba da bunkasa tattaunawa tsakanin musulmi da kirista, domin su bayar da gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya a duniya.

3821431

 

captcha