IQNA

An Bude Sabbin Makarantun Kur’ani 38 A Masar

23:47 - June 21, 2019
Lambar Labari: 3483758
Bangaren kasa da kasa, an bude sabbin makarantun kur’ani mai sarki guda 38 a fadin kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na akhbar yaum ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ce ta sanar da hakan a yau.

Bayanin ya ce a halin yanzu akwai makarantun kur’ani guda 990 a fadin kasar Masar, wadanda aka bude sua  cikin dukkanin jihohin kasar, inda yara ke samun karaun kur’ani kyauta a karkashin shirin wannan ma’aikata.

Kasar Masar na daga cikin kasashen da suka samu gagarumin ci gaba ta fuskar koyar da karatun kur’ani mai tsarki ga yara da ma matasa, inda dubban matasa suka hadace kur’ani, yayin da uma wasu miliyoyin suka lakanci tilawarsa.

 

3821107

 

captcha