IQNA

Rauhani: Karfafa Alaka Da makwabta Na Daga Cikin Siyasar Iran

22:20 - June 15, 2019
Lambar Labari: 3483739
Bangaren kasa da kasa, shugaba Rauhani na Iran a yayin ganawa da sarkin Qatar a yau Tamim Bin hamad ya bayyana cewa, daya daga cikin manufofin siyasar wajen Iran shi ne kyautata alaka da kasashe makwabta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a gefen taron ksashe mambobin na kungiyar bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen nahiyar Asia a yau a birnin Doshambe na kasar Tajikistan, shugaba Rauhani na Iran ya jaddada cewa daya daga cikin manufofin siyasar wajen Iran shi ne kyautata alaka da kasashe yankin gabas ta tsakiya baki daya.

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da sarkin Qatar Tamim Bin Hamad, inda ya jaddada masa cewa Iran ba ta da wata matsala da wata kasa a yankin, kuma a shirye take ta hada karfi da kowace kasa ta yankin gabas ta tsakiya domin gudanar da ayyuka na ci gaban al’ummomin yankin baki daya.

Ya kara da cewa,a  halin yanzu lokaci ya wuce da kasashen musulmi za su bata lokacinsu a kan abubuwan da ba su taka karya sun karya ba, ya kamata su hada kansu ne domin ta haka ne kawai za su iya samun ci gaba kuma su zama masu karfi fada a ji a duniya, domin rarrabuwar kawuna ita ce babban abin da yake jawowa musulmi tozarcin da suke gani.

Shi ma a nasa bangaren sarki Qatar tamim Bin hamad ya bayyana cewa, mahangarsu ta zo daya da Iran kan wajabcin warware duk wani sabani ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin kasashen muslmi.

Ya kara da cewa Qatar a shirye ta ci gaba da fadada alaka tare da Irana  dukkanin bangarori.

 

3819458

 

captcha