IQNA

Majalisar Sojin Sudan Ta Kori Wasu Jagororin ‘yan Adawa Daga Kasar

23:45 - June 10, 2019
Lambar Labari: 3483724
Majalisar sojojin kasar Sudan da ke rike da madafun ikon kasar a halin yanzu, ta kori wasu daga cikin jagororin ‘yan adawa daga kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a ci gaba da daukar matakai na eman ganin bayan masu adawa a Sudan da tsarin mulkin soji a kasar, majalisar sojin kasar ta dauki matakin murkushe masu gudanar da jerin gwano da zaman dirshan, ta hanyar yin amfani da karfi da kuma kama jagororin ‘yan adawar.

Bayan matakin da mahukuntan sojin na Sudan suka dauka a karshen watan Ramadan mai alfarma na yin amfani da karfi wajen tarwatsa masu zaman dirshan a gaban ginin ma'aikatar tsaron kasar da ke birnin Khartum, tare da kashe mutane 113, da kuma jikkata wasu da dama, kungiyar tarayyar Afrika ta dauki matakain korar kasar Sudan daga cikin mambobinta, har zuwa lokacin mika mulki ga hannun farar hula.

Ana ganin wannan mataki na kungiyar tarayyar Afrika yana a matsayin mayar da martani ne kan irin matakan wuce gona da iri da mahukuntan sojin na Sudan suka dauka, na kisan jama'a da kuma dakatar da duk wata tattaunawa tare da sauran bangarorin siyasar kasar.

A wani mataki na neman sulhunta bangarorin soji da kuma na farar hula da 'yan siyasa  akasar ta Sudan, Firayi ministan kasar Habsha Abiy Ahmad ya kai wata ziyara a kasar a ranar Juma'a da ta gabata, inda ya gana da bangarorin biyu, da nufin ganin an samu fahimtar juna da kuma shimfida hanyar da za ta kai ga kawo karshen zaman doya da manja a tsakaninsu.

Bayan 'yan sa'oi da kammala ganawar da firayi ministan Habasha ya yi bangaororin soji da kuma na 'yan adawa  akasar Sudan, majalisar sojin kasar ta kame wasu daga cikin jagororin 'yan adawar, lamarin da ya jawo tsunduma cikin wani mawuyacin halia  kasar, inda jama'a suka shiga yajin aiki da bore a dukkanin fadin kasar, wanda hakan yasa sojojin suka saki mutanen da suka kama, amma kuma suka kore su daga kasar.

Da dama daga cikin masana masu bin diddigin abin da yake faruwa a kasar Sudan sun yi imanin cewa, halain da ake cikia  kasar a halin yanzu yana da matukar hadari, musamman ganin yadda wasu kasahen larabawa suka shiga cikin lamarin tare da karfafa sojojin kan irin matakan da suke dauka, inda gwamnatocin Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa suke kan gaba wajen nuna goyon baya ga majalisar sojin ta Sudan tare da ba su makudan kudade, domin su ci gaba da zama kan kujerar mulki bayan hambarar da Albashir.

Abin jira a gani dai a halin yanzu shi ne, matakai na gaba da sojojin za su dauka, bayan korarar wasu daga cikin jagororin 'yan sisa a kasar, da kuma yin fatali da duk wata tattaunawa tare da 'yan adawa matukar an gindaya wasu sharudda a kanta, a daidai lokacin da suke fuskantar matsin lamba daga tarayyar Afrika da kuma sauran kasashen duniya.

3818101

Majalisar Sojin Sudan Ta Kori Wasu Jagororin ‘yan Adawa Daga Kasar

Majalisar Sojin Sudan Ta Kori Wasu Jagororin ‘yan Adawa Daga Kasar

 

 

 

captcha