IQNA

Martanin Falastianwa Kan Yarjejeniyar Karni

22:31 - May 20, 2019
Lambar Labari: 3483658
Bangaren kasa da kasa, hukumar kwarya-kwaryan cin gishin kai ta Falastinawa ta bayyana abin da ake kira da yarjejniyar karni da cewa manufarta ita ce bautar da Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin tashar Almanar ya bayar da rahoton cewa, hukumar Falastinawa ta mayar da martani dangane da zaman kasar Bahrain kan yarjejeniyar karni, inda tace ba abu ne mai yiwuwa ba.

Nabil Abu Rudaina babban jami’I a gwamnatin Falastinawa ya bayyana cewa, ba a shirye suke su amince da abin da yajejeniyar karni ta kunsa ba, domin kuwa ana nufin sake mayar da su karkashin mulkin mallaka na Isra’ila ne ta wata sabuwar hanyar yaudara.

Wasu na ganin cewa da zaran an bayyana cewa an rattaba hannu kan yerjejeniyar karni ko sulhun karni tsakanin Palasdinawa da kuma yahudawan sahyoniya, to koma ya kare abubuwa zasu tafai lafiya a yankinn gabsa ta tsakiya.

Kuma suna ganin Amurka ce zata zama gwarzon karni don ta sami nasara cimma wannan yerjejeniyan.

Sai dai gaskiyar lamarin bah aka bane, ba wai kawai Amurka da Isra’ila bas a son tabbatar da adalci da kuma zaman lafiya na gaskiya a gabas ta tsakiya ba, sai dai basu ma kama hanyar tabbatar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya ba, misali a cikin shirin:

1 - Za’a kafa kasar Palasdinu a yankin, amma a abinda yake kasa shi ne Israela tana mamaye da dukkan yankunan da aka ce za’a kafa kasar ta Palasdinu.

2 - Sannan idan shugaban Palasdinawa ya ki sanya hannu a kan yerjejeniyarAmurka zata yanek dukkan tallafi na kudaden da take bawa gwamnatinsa har sai ta fadi, ko kuma ta amince das a hannu.

3 - idan kuma ya sanya hannu, sannan kungiyar Hasar da kuma jahadul islami suka ki amincewa sai Israel ta yi dirar mikakiya a kan shuwagabannin Palasdinawa da suka ki amincewa da sulhu ta yi ta kasha su, Amurka kuma na bayanta.

4 - batun dakatar da tallafin da Amurka da sauran kasashen suniya suke bawa Palasdinawa yana gudana tun watannin da suka gabata, wannan bai hanasu ci gaba da gwagwarmaya da yahudawan Israela ba.

5 - Yarjejeniyar Karni ba sulhu ba ce kuma ba mai aiwatuwa ba ce. Sannan ko wadanda suka shirya shi wato Amurka da Israela basu dauki shi a matsayin sulhu ba.

6 - Wannan shirin yana nufin samar da sabbon shuwagabannin kasashen Larabawa wadanda zasu yi biyayya ga kasar Amurka da Isra’ila.

7 - Wannan shirin na Amurka a wajenta ba a bin tattaunawa mane, sai dai bin umurni ga dukkan kasashen yankin, wacce ta ke zata dandana kudanta.

8 - Amurka ta fara aiwatar da wannan shirin tun shekara ta dubu das ha bakawai, inda ta shelanta quds a matsayin headquatan Isra’ila.

9 - ta kwace tuddan Golan ta mallakarwa Isra’ila, wannan yarjejeniyar Palasdinawa zasu rasa kome, hatta hakkin komawa kasarsu basu da shi, kasashen larabawa ne zasu san yadda zasu yi su maida yan gudun hijirar Palasdinawa su zama yan kasa a inda suke zama har abada.

10 - shirin sulhun karni ko yerjejeniyar karni baya nufin samar da zaman lafiya a gabas ta tsaya tun farko.

11 – An tilastawa shuwagabannin larabawa amincewa da dukkan Amurka ta yanke, sansan dukkaninsu su zama makiyan jamhuriyar musulunci su taimakawa Amurka da kawayenta don yakarta.

 

3813168

 

captcha