IQNA

An Kai Wasu hare-hare A kan Masallatai 5 A Birmingham

23:42 - March 23, 2019
Lambar Labari: 3483485
A ci gaba da nuna wa musulmi kyama da wasu ke yia kasar Birtaniya, an kai wasu hare-harea kan wasu masallatai guda biyar a garin Birmingham.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin wani bayani da ya fitar a jiya, ministan harkokin cikin kasar Birtaniya Sajid Jawid ya bayyana cewa, hare-haren da aka kai kan masallatan musulmi a birnin Birmingham babu abu ne da za a aminta da shia  kasar ba.

Ya ce ko shakka babu yadda kyamar musulmi ke karuwa  akasar abu ne mai matukar daga hankali, domin kuwa a cewarsa, kasar Birtaniya kasa ce wadda take kan gaba wajen rayuwa  atsakanin mabuya addinai daban-daban a cikin zaman lafiya ba tare da kyamar juna ba.

A kan haka ya ce za su dauki dukaknin matakan da suka dace domin shiga kafar wando daya dag amsu irin wanann akida ta kyamar wani bangaren al'umma saboda addini ko akida.

Tun a daren Alhamis da ta gabat ce wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari kan wasu masallatai a cikin a cikin garin Birmingham, tare da farfasa tagogi da kuam lalata kayayyakin masallatan.

3799506

 

 

 

 

 

captcha