IQNA

Martanin Cibiyar IHR A Birtaniya Kan Take Hakkokin Musulmi A Kasar

23:21 - March 19, 2019
Lambar Labari: 3483472
Cibiyar da ke kula da kare hakkokin musulmi a kasar Birtaniya, ta zargi gwamnatin kasar da yin tafiyar hawainiya wajen kula da lamarin musulmin kasar yadda ya kamata.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Wannan ya zo ne a cikin wata wasika da cibiyar ta aikeawa ministan harkokin cikin kasar Birtaniya, biyo bayan harin ta’addancin da aka kai kan musulmia  kasar New Zealand a  ranar Juma’a da ta gabata, inda cibiyar ta bayyana cewa, ayyukan kyamar musulmi na ci gaba da karuwa a cikin Birtaniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa, a cikin ‘yan lokutan baya-bayan nan abubuwa da daa sun faru a cikin kasar ta Birtaniya, da nuni da irin yadda kin jinni da kyamar musulmi suka karu a kasar, tare da yin ishara da harin birnin London da aka kai a shekara ta 2017, da kuma yadda masu tsatsauran ra’ayin kin jinin musulmi suka kasha wani musulmi a birnin Birmingham, da kuma kai farmaki a kan masalatai da wuraren ibadar musulmi da suka yi ta faruwa a yankuna daban-daban na Birtaniya.

Cibiyar ta ce abin tambaya a nan, wace irin raw ace gwamnatin Birtaniya take takawa domin kare rayukan musulmi da dukiyoyinsu da wuraren ibadarsu da mutuncinsu da kuma ‘yancinsu na addini?

A daya bangaren wasikar ta tabo batun kasafin kudi da ake warewa domin bayar da kariya ga wuraren ibada na addinai daban-daban a kowace shekara a Birtaniya, inda ministan harkokin cikin gida na kasar Sajid Jawid ya ce a shekarar da ta gabata an ware kudi Fn dubu 600 domin kare wuraren ibada na yahudawa  afadin kasar, amma a shekarar bana abin da aka ware domin kare wuraren ibadar yahudawa a Biratniya ya kai fan miliyan 14, yayin da kuma aka ware fan miliyan 2.4 domin bayar da kariya ga wuraren ibada da cibiyoyi na mabiya sauran addinai daga cikin har da mabiya addinin musulunci.

Bayanin ya ce wannan mataki da gwamnatin Birtaniya ta dauka babau adalci a cikinsa, domin uwa adadin musulmin da suke cikin kasar, ya ninka adadin yahudawan da suke cikin kasar sau goma, wanda hakan ke tababtar da cewa ana nuna wa musulmi wariya da banbanci tsakaninsu da wasu a kasar.

Cibiyar ta ce, tana son Karin bayani dangane da dalilan da suka sanya jami’an tsaron ‘yan sand aba su bin kadun abubuwa da dama da suke faruwa nacin zarafin musulmi saboda addininsu a kasar, da hakan ya hada da cin zarafin mata masu sanye da suturar mususuluncia a wasu lokuta, ko kuma yin izgili da kalaman batunci ga addinin muslunci a lokacin da musulmi suka shiga wasu wuraren, kamar tashoshin jiragen kasa na karkashin kasa da sauransu, da sauran abubuwa na cin zarafin har ma daduka a wasu lokuta, wanda kuma jami’an tsaron Birtaniya ba su cika bayar da muhimmanci ga irin wadannan lamurra ba kamar yadda ya kamata.

Daga karshe cibiyar ta ce tana son samun wadannan bayanai daga bangare ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Birtaniya, domin kuwa bisa ga bayanin wanann ma’iakta ne za ta dora, domin daukar matakai nag aba.

3799032

 

captcha