IQNA

Shiri Kan Isar Da Sakon Muslunci A Cibiyar Zahra Da Ke Canada

23:51 - January 15, 2019
Lambar Labari: 3483314
Bangaren kasa da kasa, cibiyar musulmi ta Az-zahraa Islamic Centre da ke birnin Richmond na kasar Canada, za ta gudanar da wani shiri bayyanawa mabiya addinai yadda ake ibada a muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shirin mai taken A Journey to Islam wato tafiya zuwa ga muslunci, zai mayar da hankali ne wajen yin bayani kan abubuwa da suka shige ma wasu mabiya addinai duhu dangane da musulunci.

Za a fara gudanar da shirin a ranar 26 ga wannan wata na Janairu, kuma zai ci gaba har tsawon wasu kwanaki kafin aka kammala shi.

A taron za a gayyaci mabiya addinai daban-daban domin su halarci wurin, inda musulmi za su gudanar da ayyukan ibadarsu kamar salloli na farilla da sauransu, da kuma bayanai kan hakikanin addinin mulsunci da kuma mahangarsa kan sauran addinai.

Haka nan kuma za a amsa tambayoyi na mutanen da aka gayyata dangane da abin da suke son sani a kan addinin muslucni, domin su ji daga bakin musulmi kai tsaye.

Babbar manufar shirin dai ita ce kusanto da fahimta da karfafa zaman lafiya a tsakanin musulmi da sauran mabiya addinai, tare da nunawa duniya cewa hakanin addinin muslucni yana tattare ne da zaman lafiya da girmama dan adam.

3781561

 

 

 

captcha