IQNA

An kame Wasu 'Yan Ta'addan Daesh A kasar Lebanon

22:04 - January 10, 2019
Lambar Labari: 3483303
Jami'an tsaron kasar Lebanon sun samu nasarar cafke wasu 'yan ta'addan Daesh su a kasar a lokacin da suke shirin kai munanan hare-hare.

Shafin yada labarai na Sadl Balad ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron kasar Lebanon sun kame 'yan ta'addan ne wadanda suke shirin kai wasu munanan hare-harea  kan wasu cibiyoyi na gwamnati da kuma na sojia  kasar.

Bayanin ya ce kame wadannan mutane ne zai taimaka matuka waje kame wasu wadanda ake nema a kasar da suke da alaka da kungiyoyin na 'yan ta'adda, wadanda suka kai wasu hare-hare a  kasar a shekarun baya.

Jami'an tsaron kasar ta Lebanon sun sun ce, daya daga cikin 'yan ta'addan da aka kame, shi ne ya bude wata hanya ta yanar gizo, inda ake yin rijistar 'yan ta'addan ta hanyar yanar gizo daga kasashen duniya daban-daban, musamman ma daga nahiyar turai, domin kai su zuwa kasashen Syria da Iraki domin yin abin da suke kira jihadi.

Daga farkon rikicin Syria 'yan ta'adda sun mayar da kasar Lebanon hanyar wucewa zuwa Syria, musamman wadanda suke fitowa daga kasashen larabawa na yammacin Afrika, kafin daga bisani mahukuntan kasar suka dauki kwaran matakai kan hakan.

 

3780060

 

  

 

 

captcha