IQNA

Aljeriya Ta Bukaci Da A Gyara Tsarin Kungiyar Kasashen Larabawa

23:48 - October 08, 2018
Lambar Labari: 3483033
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Ajeriya ta bukaci da a yi wa kungiyar kasashen larabawa garambawul.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Abdulqahir Musahil ministan harkokin wajen kasar Aljeriya ya bayyana cewa; suna da bukatar a gudanar da sauye-sauye a  cikin tsarin tafiyar da kungiyar kasashen larabawa.

Yace babban abin da suke bukata shi ne, kungiyar ta zama mai cikakken ‘yanci wajen daukar dukkanin matakin da take ganin ya dace, maimakon yadda kungiyar take a halin yanzu.

Inda y ace kungiyar ba ta da iko zartar da wani abu sai abin da wasu kasashe suke bukata, ta hanyar yin amfani da wasu kasashen larabawan masu karfin fada a ji a cikin kungiyar.

A cikin shekarar 2005 da aka gudanar da taron kungiyar a kasar Aljeriya, gwamnatin kasar ta gabatar da shawara kan yin canje-canjea  cikin tsarin kungiyar, da hakan ya hada yin shugaba na karba-karba, maimakon takaita shugabancin da kasar Masar kawai.

3754161

 

 

 

 

captcha