IQNA

Sheikh Abdulmumin Dalahu:

Takunkumi Yana Kara Wa Kasar Iran Karfi Ne

23:48 - October 06, 2018
Lambar Labari: 3483029
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Abdulmumin Dalahu a lokacin da yake ganawa da karamin jakadan Iran a Ghana ya bayyana takunkumin Amurka kan Iran da cewa yana karawa Iran karfi ne.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a  lokacin da Sheikh Abdulmumin Dalahu daya daga cikin manyan malaman kasar Ghana yake ganawa da karamin jakadan Iran a Ghana Muhammad Hassan Ipikchi, ya bayyana takunkumin Amurka kan Iran da cewa bai zai taba rusa Iran ba.

Shehin malamin ya ce tun bayan juyin juya halin muslunci Iran ta tabbatar wa duniya cewa takunkumi baya kara mata komai sai ci gaba da kuma dogaro da kanta, wanda a cewarsa Iran ta kai matsayinta na yanzu sakamakon takunkuman da aka yi ta kakaba mata ne.

Daga karshe ya mika sakon ta’aziyya ga al’mmar Iran baki daya dangane da harin ta’addancin da aka kai a birnin Ahwaz a kwanakin baya, tare da bayyana hakan da cewa aiki ne na dabbanci.

3753247

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha