Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga Kamfanin dillancin labaran Sputnik cewa, sojojin Masar sun fitar da sanarwa da ke cewa, a wani farmaki da suka kaddamar a jiya a wata maboyar 'yan ta'adda a yankin Sinai, sun samu nasarar halaka 'yan ta'addan takfiriyyah 15 tare da jikkata wasu da dama.
'yan ta'addan masu alaka da kungiyar Daesh sun shelanta yaki kan gwamnatin kasar Masar ne tun bayan hambarar da Muhammad Mursi daga kan karagar shugabancin kasar ta Masar.
A ranar Talata da ta gabata ma sojojin Masar sun sanar da kashe Abu Hamza Almaqdidi, daya daga cikin manyan kwamandojojin 'yan ta'addan Masar masu alaka da alqaeda.