Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai sarki ta duniya a karo na arbain a kasar saudiyya da ake a kowace shekara.
Wannan gasa dai kimanin makaranta da mahardata 115 ne daga kasashen duniya 82 suke samun halartar ta, kuma an agudanar da ita ne a bangarori hudu, da suka hada da harda, kira’a da tajwidi da kuma tafsiri.
An gudanar da taron share fage a jiya, inda wadanda suka samu suka tsallake za su kai ga sauran matakai nag aba, kuma za a kammala gasar ne bayan kwanaki hudu a masallacin manzon Allah da ke Madina munawwara.
Sheikh Abdallah bin Ahmad Alfaqih, Walid Bin Huzam Alatibi, Abdullah bin Ata’allah alhussaini su ne manyan alakalan mataki na farko na gasar.