Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ana shirin gudanar da taron makokin shahadar Imam Sajjad (AS) a birnin Moscow na kasar Rasha a ranar Asaba mai zwa.
Kwamitin masalacin khatamul anbiya ne y dauki nauyin shirya wannan taro, wanda zai samu halartar Hojjatol Islam Saber Akbari wakilin wilayatol faqih a Mosco, da kuma wasu daga cikin malamai.
Za a gabatar da jawabai a wurin dangane da matsayin Imam Sajjad, da kuma iin darussan da suke a cikin rayuwarsa mai albarka.
A ranar 25 bisa wasu ruwayoyi Imam Sajjad ya yi shahada, wanda kuma mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah suna gudanar da tarukan tunawa d shahadarsa.