IQNA

Sabon Shirin Gwamnatin Aljeriya Dangane Da Limamai Masu Yada Tsatsauran Ra'ayi

22:56 - October 03, 2018
Lambar Labari: 3483025
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar Aljeriya ta tanadi wani sabon shiri na sanya ido kan dukkanin limaman masallatan kasar, domin kawo karshen yada tsatsauran ra'ayi da rarraba a tsakanin musulmin kasar.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Sadal balad ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar ta Aljeriya ta sanar da cewa, bisa la'akari da tasirin da limamai suke da shi a masallatan da suke gabatar da huduba ko jawabai, wannan ya bai wa wasu damar yada akidu na kafirta musulmi da kawo rarraba da kin juna a tsakanin musulmi.

A kan gwamnatin kasar ta ce ta bullo da wasu sabbin tsare-tsare da suka shafi yadda za a rika tafiyar da masallatai da kuma hudubobin da ake yi, ta yadda za su zama daidai da abin da yake maslaha ta addini da zamantakewar al'umma, tare da hana duk wani wa'azi ko huduba da ake sukar ko kafirta wani bangaren musulmi.

Kasar Aljeriya dai tana daya daga cikin kasashen larabawan arewacin nahiyar afrika suke fama da matsalolin kungiyoyi masu da'awar jihadi da suke dauke da akidar salafiyya, wadanda sukan hade da kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya irin su alkaida da Daesh.

3752436

 

captcha