Kamfanin dillancin labaran iqna, Bisa sanarwar da ofishin babban jami’i mai kula da tsare-tsare na jami’ar ya bayar, daga cikin sabin kwasa-kwasan akwai koyar da ilimin tarbiyya da kuma ilimin zamantakewar al’ummomi.
Jami’ar muslunci ta kasar Ghana dai tana daga cikin jami’oin da suke samun karbuwa a tsakanin al’ummar kasar har ma da wasu daga cikin al’ummomin kasashen Afirka ta yamma.
Wannan jami’a dai tana kokarin ganin ta koyar da ilmomi da suka danganci muslunci a zamanance, kamar yadda kuma take koyar da wasu ilmomin daidai da sauran jami’oi domin tsarinta ya tafi bai daya a wasu bangarorin da sauran jami’oin kasar a hukumance.
Kasar Ghana dai tana daya daga cikin kasashe masu tasiri a yankin yammacin nahiyar Afirka ta fuskoki da dama, da suka hada hard a bangaren ilimi.