IQNA

Saudiyya Ta Kashe Yara 39 A Yemen

23:47 - August 09, 2018
Lambar Labari: 3482877
Bangaren kasa da kasa, wani harin sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen, ya yi sanadimin mutuwar yara 'yan makaranta a kalla 39 tare da jikkata wasu mutane 48 na daban a arewacin kasar ta Yemen.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an kai harin ne kan wata motar bus dake dauke da yara a lardin Dahyan, dake arewacin Saada, kuma mafi yawancin yaran da lamarin ya rutsa dasu 'yan sakanin shakara goma zuwa sha hudu ne.

Kafin hakan dama kungiyar agaji ta kasa da kasa, dake bada taimaka ga asibitin yankin ta ce harin ya yi ajalin mutane da dama galibi yara, wanda a cewarta ya kamata a dinga kare fararen hula a lokutan yaki.

Ita kuwa a nata bangare, wakliyar asusun kula da yara na MDD ta ce ta kadu matuka da samun wannan labarin.

Wata sanarwa da kawancen da Saudiyya ke jagoranta kan yakin kasar ta Yemen ya amince da kai harin, tare da kare harin da cewa yana bisa ka'ida, kuma daidai da dokikin kasa da kasa.

3737224

 

 

captcha