IQNA

Zaman Makokin Shahadar Sayyida Zahra Tare Da Halartar Jagora

22:13 - February 19, 2018
Lambar Labari: 3482409
Bangaren siyasa, An fara gudanar da zaman makokin shahadar Sayyida Fatima Zahra amincin Allah ya tabbata a gare ta, wanda jagoran juyin juya halin musulunci ya halarta a Husainiyyar Imam Khomeni (RA) da ke birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin intanet na ofishin jagoran, Ayatollah Sayyid khamenei ya ba da bayanin cewa; a daren jiya ne aka fara zaman makokin, tare da halartar jagora, da wasu daga cikin manyan jami’ai da malamai da kuma dubban al’ummar gari.

Hottatol Islam Siddiqi gabatar da jawabi a wurin. Inda ya tabo wasu daga cikin falalar da Allah ya kebance ta da su, daga ciki kuwa har da kasancewarta wacce manzon Allah ya fi so a tsakanin dukkanin halittun Allah.

Tana da matsayi madaukaki a wurin Allah, ta yadda Allah madaukakin sarki ya sanya dukkanin limaman Ahlu bait (AS) goma sha daya da su zamo ‘ya’yansu ne, da jikokinsu ita da mijinta Imam Ali (AS).

Daga karshe an karanta wasu baitotocin makokin shahadarta, amincin Allah ya tabbata a gare ta.

 

3692794

 

 

 

 

 

 

 

captcha