IQNA

Martani Kan Matakin Trump Na Amincewa Da Quds A Matsayin Birnin Sahyuniyawa

23:07 - December 07, 2017
Lambar Labari: 3482178
Bangaren kasa da kasa, Matakin shugaban Amurka Donald Trump na ayyana Qudus a hukumance babban birnin yahudawan mamaya na Isra'ila na ci gaba da shan suka daga kasashen duniya, in banda mahukuntan yahudawan da suka bayyana matakin a mastayin wani babban abun tarihi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jim kadan bayan sanarwar, babban sakatare na MDD, Antonio Guteress ya yi Alla-wadai da matakin da shugaba Donald Trump ya dauka, inda ya ke cewa ta hanyar tattaunawa ne kawai za a warware matsalar, baya ga bayyana halin da ake ciki a matsayin zaman zullumi wanda babu wani zabi da ya rage illah a samar da kasashe biyu.

Da yake mayar da martani, Mahmud Abbas, ya ce, a wannan matakin da Amurka ta tauda ta rushe duk wani shiri da ake da shi na samar da zaman lafiya, tare da ayyana kawo karshen yarjejeniya ta tsawan shekaru da aka cimma.

Kungiyar LPO mai fafatukar kwato 'yancin Palasdinawa ta bakin shugaban ta, Saeb Erekat, ya ce Trump ya ruguza hanyar kaiwa ga samar da kasashe biyu, kana kuma ya fidar da Amurka daga duk shirin samar da zaman lafiya.

Ita kuwa kungiyar fafatukar Islama ta Palasdinawa Hamas cewa ta yi, shugaban Amurka ya bude ''kofofin jahannama ga kadarorin Amurka a yankin'' 

Ismaïl Raduane, wani jigo a kungiyar ta Hamas ya bayyanawa manema labarai a yankin Gaza cewa, dole ne kasashen larabawa dana musulmi su farka su kuma katse duk wata hulda ta siyasa da tattalin arziki da ofisoshion jakadancin Amurka tare da korar jakadanta.

Ma'aikatar hakokin wajen Jamhuriya musulinci ta Iran, ta fitar da wata sanarwa inda ta yi alla-waidai da abunda ta danganta da keta yarjejeniyar kasa da kasa karara, wacce kuma zata iya tado wani sabon boren ''Intifada'' 

Sanarwar ta ce matakin na Trump marar kan-gado zai rura wutar rikci da hadasa wata sabuwar fitina da tsatsauran ra'ayi.

Iran ta ce birnin Qudus wani babban bangare ne na Palastinu. 

Kasar Jodan ta ce matakin Trump na amuncewa da Qudus babban birnin yahudawan Isra'ila da kuma mayar da ofishin jakadancin Amurkar zuwa birnin, keta dokokin kasa da kasa ne da yarjejeniyar MDD, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar ta Jodan Mohammed Moumenie.

Saudiyya wacce ke dasawa da gwamnatin Amurka ita ma ta fitar da wata sanarwa, inda ta nuna takaici  da abunda ta kira rashin adalci ga al'ummar Palastinu.

Sanarwar da masarautar kasar ta fitar ta ce dama ta yi kashedi akan mummunan abunda irin wannan matakin zai haifar, tare da bukatar Amurka data canza wannan shawara data sabawa dadaden yancin al'ummar Palastinu a birnin Qudus.

Saudiyya ta ce wannan koma baya ne ga yunkurin Amurka na samar da zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta danganta matakin shugaba Trump da rashin tunani da rashin sanin abunda ya kamata, tana kuma mai yin tir da matakin wanda ta ce ya sabawa dokokin kasa da kasa a cewar ministan harkokin wajen kasar Mevlut Cavusoglu a shafinsa na Twitter.

Dama kafin hakan shugaban kasar Recep Erdogan ya ce matsayin Qudus jan layi ne da bai kamata a kai gare sa ba.

Tun daga birnin Alges na kasar Aljeriya inda ya ke ziyara, shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce abun takaici ne matakin na Trump kan birnin Qudus, tare da kira a kaucewa tashin hankali.

Mista Macron ya jaddada goyan bayan Faransa da Turai kan samar da kasashen Palastinu da Israila kusa da kusa da zasu kasance cikin zaman lafiya amma a cikin iyakokin da kasashen duniya suka amunce dasu a msatyin kuma Qudus babban birnin kasashen biyu.

Baya ga wadanda kasashe da hukumomin da gwamnati, akwai kasashen Biritaniya, Canada, Italiya, Labanon, Siriya, Tunisiya, Marocco, Aljeriya, Senegal, tarayya Turai da ta AFrika da su ma suka yi tir da matakin.

Kwamitin tsaro na MDD dai ya kira wani taraon gaggawa a gobe juma'a, a yayin da kungiyoyin kasashen larabawa da na musulmi OIC suma suka kira wani taro kafin nan da karshen wannan mako don tattauna wannan batu.

A kasashen Afrika na yankin kudu da hamadar Sahara shiru dai ake ji har zuwa wayewar safiyar sanar da matakin na Trump kan ayyana Qudus babban birnin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila.

3670364

 

 

 

 

 

 

captcha