IQNA

Dole Ne Musulmi Su Mike Domin Takawa Amuka Da Isra’ila Burki

22:50 - December 07, 2017
Lambar Labari: 3482176
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya ja kunnen Amurka dangane da batun mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Qudus yana mai cewa wajibi ne kasashen musulmi su hada kansu waje guda don tinkarar wannan lamari.

Dole Ne Musulmi Su Mike Domin Takawa Amuka Da Isra’ila BurkiKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cwa, Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da takwararsa na kasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan inda ya ce a irin wannan yanayi ya zama wajibi kasashen musulmi da al'ummominsu su hada kansu waje guda da kuma daukar matakin da ya dace wajen tinkarar wannan haramtacciyar matsaya kana kuma mai hatsarin gaske da Amurka ta dauka.

Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa lamarin Palastinu da kuma fada da irin zaluncin da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi wa Palastinawa shi ne babban lamarin da ke gaban duniyar musulmi.

A jiya ne dai shugaban Amurkan Donald Trump, cikin wani jawabi da yayi, ya bayyana birnin Qudus din a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma sanar da shirin Amurkan na mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin na Qudus, lamarin da ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na duniya.

3670340

 

 

 

 

 

captcha