IQNA

Bayanin Addinin Musulunci Ga Wadada Ba Musulmi Ba

23:39 - October 12, 2017
Lambar Labari: 3481992
Bangaren kasa da kasa, makarantar Dodalas a kasa Birtaniya ta gayyaci wani mai fadakarwa ta addinin muslunci domin yin bayani kan muslunci ga dalibai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nwemail cewa, wannan makaranta ta kan shirya taruka na tarbiya da kuma zamatakewa , inda akan kira masana domin yin bayani ga dalibai, a wannan mako an gayyacin Imran Kotwal wani musulmi domin yin bayai.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa ga dalibai, ya yi ishara da matsalolin da ake fama da su wajen rashin fahimtar musulmi da kuma yi msuu hukunci sabanin yadda suke.

Daga ciki kuwa har da yadda wasu mutane da dama a kasar da ma wasu kasashen duniya suke kallon musulmi a matsayin wasu mutae masu son tashin hankali.

Malamin ya yi bayani kan sahihin tafarki da kuma koyarwa irin ta addinin muslunci, wadda ta ginu a kan girmama dan adam da kare hakkokinsa, da kuma zaman lafiya da fahimtar tare da sauran al’ummomi.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda wasu amsu kaataciyar fahimta suk bata snan addinin musluni ta hanyar akata ta’addaci da sunan wannan addini mai tsarki, inda ya ce irin wadannan mutane basu suna wakiltar muslunci ko musulmi ba ne.

3652045

captcha