IQNA

Gasar Kur'ani Ta Kasa da Kasa A Yankin Port Said

23:15 - October 07, 2017
Lambar Labari: 3481975
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da gasar kur'ani mai tsarki mai taken faizun a lardin Port said na kasar Masar a cikin 'yan watanni masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wannan gasa wadda aka fara gudanar a matsayi na kasa da kasa, a shekarar da ta gabata, za ta ci gaba da gudana akaro na biyua wannan mataki.

Gwamnan lardin Adil Gadban ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu an kammala dukkanins hirye-shiryen da suka kamata domin aiwatar da wannan shiri, inda yanzu haka ana cikin gudanar da wata gasar ta share fage.

An dauki tsawon shekaru goma sha hudu ana gudanar da wannan gasa amma a matsayi na cikin gida kawai a yankin na Port said, inda mahardata daga dukkanin bangarori na kasar Masar suke halartar gasar.

Amma a halin yanzu wannan gasa ta tashi daga matsayin gasar hardar kur'ani ta cikin gida ta koma gasa ta duniya, inda mahardata daga kasashen duniya suke halarta kamar yadda aka yi a shekarar da ta gabata, kuma a bana ma da yardarm Allah za a gudanar.

3649846


captcha